
Mutum daya ne ake fargabar ya mutu bayan wata tankar mai dauke da man fetur ta fado kan wata motar jan ababen-hawa a Otto Wharf, kan titin Apapa – Oshodi Expressway, Mile 2, Legas.
Hukumar kashe gobara ta jihar Legas ta shafinta na Twitter a yau Lahadi ta bayyana cewa, hatsarin ya afku ne da sanyin safiya, yayin da motar dakon mai ta nufi Oshodi daga Apapa, inda ta yi lodin dizel.
An ceto daya daga cikin wadanda hadarin ya rutsa da su ya ji rauni amma yana raye.