
Hukumar Kwastam ta Ƙasa, NCS, a yau Litinin ta buɗe kan iyakar Kamba da ta haɗa kasar da jamhuriyar Nijar a kan hanyar Kebbi a hukumance.
Gwamnatin tarayya, ta wata sanarwa da hukumar NCS ta bayar a ranar Juma’a ta ba da umarnin sake buɗe ofisoshin kan iyaka a Idiroko (Ogun); Jibiya (Katsina) Kamba (Kebbi) da kuma Ikom (Cross River).
Gwamnati ta rufe manyan kan iyakokin kasar ne a wani ɓangare na ƙoƙarin daƙile yaɗuwar annobar korona da dakile fasa-ƙauri domin bunkasa noman shinkafa da sauran amfanin gona na cikin gida.
Yayin da ya ke jawabi wajen buɗe kan iyakar a hukumance a Kamba, shugaban hukumar kwastam na jihar Joseph Attah, ya bayyana fatansa cewa iyakar za ta buɗe wani sabon shafi na hulɗar tattalin arziki tsakanin ƙasashen biyu.
“Sake bude kan iyakar ba wai yana nufin an sake buɗe hanyar haramtaccen kasuwanci ba ne, a’a, an buɗe ne don amfanar juna ta fuskar tattalin arziki tsakanin kasashe biyu na kungiyar raya tattalin arzikin kasashen yammacin Afirka (ECOWAS).
“An sake bude kan iyaka don kasuwanci, da kuma inganta tattalin arzikinmu, amma ku lura cewa dokar hana shigo da shinkafa, kaji da sauran kayayyakin da aka hana shigowa da su har yanzu tana nan kuma rundunar da ke aikin sintiri za ta ci gaba da aiwatar da ita,” in ji shi