
Wata fashewa mai girma a kusa da birnin Chittagong na ƙasar Bangladesh ta kashe akalla mutum 32.
An bayar da rahoton cewa ɗaruruwan mutane ne suka jikkata sakamakon fashewar, wadda ta faru a bayan wata ma’ajiyar man fetur da ke Sitakunda.
Hukumomi sun ce ma’aikatan kashe gobara na cikin wadanda suka mutu.
Wakiliyar BBC ta ce asibitoci a yankin sun cika maƙil suna neman a ba su gudummawar jini, sannan mahukunta na gargaɗin cewa ana sa ran adadin wadanda suka mutu zai karu.
Har yanzu dai ba a bayyana musabbabin tashin gobarar ba amma ana tunanin an ajiye sinadarai ne a cikin wasu daga cikin kwantenonin da ke wurin.