
Gwamnatin Tarayya ta bayyana cewa ayyukan ta’addancin da ke faruwa a yankin Arewacin Nijeriya, ciki har da harin da aka kai kan jirgin kasan Abuja zuwa Kaduna, wasu ƴan bindiga ne da su ka ƙulla ƙawance da ƴan kungiyar Boko Haram ne ke aikata wa.
Ministan Tsaro, Bashir Magashi, da takwaransa na yada labarai da al’adu, Lai Mohammed, ne suka bayyana hakan a lokacin da su ke zantawa da wakilan yaɗa labarai na gidan gwamnatin tarayya bayan taron majalisar zartaswa na wannan makon.
A cewar Ministocin, duk da cewa hukumomin tsaro na ci gaba da aiki tukuru domin bayyana kungiyar da ta kai harin, rahotannin farko-farko sun nuna cewa ƙawancen ƙungiyoyin ƴan ta’adda ne ke aikata wa.
Magashi ya ce: “A gaskiya ina ganin shugabannin tsaro suna bakin kokarinsu wajen bankado wadanda ke da hannu a ciki, kuma nan ba da jimawa ba za mu gaya muku wadanda ke kai wadannan hare-hare.
“Dukkanin hare-haren da aka kai a Jos da Kaduna, za mu zo mu bayyana wa jama’a hakikanin abin da ke faruwa da kuma kokarin da muke yi na ganin an dakatar da duk wadannan ayyukan gaba daya.
“A gaskiya muna kan lamarin, muna yin shiri sosai kuma za mu fitar da shi da wuri.”
Shi kuma Mohammed ya kara da cewa “Abin da ke faruwa a yanzu shi ne akwai wani irin musabaha mara kyau tsakanin ‘yan bindiga da mayakan Boko Haram.
“Rahotanni na farko na abin da ya faru a harin jirgin kasa na Kaduna ya nuna cewa akwai wani irin hadin gwiwa tsakanin ‘yan bindiga da ‘yan ta’addan Boko Haram da aka fatattake daga yankin Arewa maso Gabas. Zan iya fada muku da kwarin guiwa cewa Gwamnatin Tarayya ce ke kan wannan al’amari.”