Home Labarai Ƴan fashin jeji sun saki ƴaƴan tsohon Akawun Zamfara bayan sun shafe watanni 7 a tsare

Ƴan fashin jeji sun saki ƴaƴan tsohon Akawun Zamfara bayan sun shafe watanni 7 a tsare

0
Ƴan fashin jeji sun saki ƴaƴan tsohon Akawun Zamfara bayan sun shafe watanni 7 a tsare
‘Yan fashin jeji sun sako ƴaƴan Abubakar Furfuri, tsohon Akanta-Janar (AG) da suka sace a jihar Zamfara.
Rahotanni sun ce an sace ƴan matan ne su biyar daga gidansu da ke Furfuri,  Ƙaramar Hukumar Bungudu, a watan Maris.
A cikin watan Oktoba, an ce masu garkuwa da ƴan matan sun fitar da wani faifan bidiyo da ke nuna U dauke da bindigogi tare da yi musu barazanar maida su ƴan fashin jeji idan har ba a biya kudin fansa da suka nema ba.
Sai dai kuma mai baiwa gwamnan Zamfara shawara na musamman kan wayar da kan jama’a, Zailani Bappa ya tabbatar da sakin su. Ya ce an mika ƴan matan ga gwamna Bello Matawalle a jiya Litinin.
A cewar Bappa, hadin gwiwar ƴan sanda da sauran jami’an tsaro ne ya sanya a ka samu nasarar kubutar da ƴan matan ba tare da wata matsala ba.
A nashi ɓangaren, Matawalle ya yaba wa jami’an tsaro bisa kokarin da suke yi, ya kuma bukace su da su kawo karshen ‘yan fashin jeji a jihar.
Gwamnan ya kara da cewa bayanan sirri sun nuna cewa an yi nasarar kuɓutar da  ‘yan matan tare da taimakon masu ba da bayanan sirri daga ƴan uwa ko kuma makusanta.