Home Ƙasashen waje Fasinjoji 132 sun mutu a haɗarin jirgin sama a China he

Fasinjoji 132 sun mutu a haɗarin jirgin sama a China he

0
Fasinjoji 132 sun mutu a haɗarin jirgin sama a China he

 

Jirgin China Eastern Airline mai ɗauke da fasinjoji 132 ya yi haɗari a kusa da birnin Wuzhou da ke Guangxi a kudancin China a yau Litinin.

Hukumomin sufurin sama me su ka tabbatar da faruwa haɗarin.

Wata kafar yada labarai ta kasar ce ta fara fitar da labarin haɗarin, inda ta ce mutane 133 ne su ka rasu.

A halin yanzu dai babu wani baya i a kan fasinjojin da kuma sanadiyyar haɗarin.

Rahotanni sun baiyana cewa jirgin, Boeing 737-800NG, mai MU5735 ya 5aso ne da ga Kunming a lardin Yunnan zuwa Guangzhou da ke lardin Guangdong.

Rahotanni sun ƙara da cewa ma’aikatan jin-ƙai na kan hanyar su ta zuwa ceto a inda jirgin ya fadi.