Home Labarai Fasinjoji 12 sun ƙone ƙurmus a haɗarin mota a Kano

Fasinjoji 12 sun ƙone ƙurmus a haɗarin mota a Kano

0
Fasinjoji 12 sun ƙone ƙurmus a haɗarin mota a Kano

 

Mutane 12 ne su ka ƙone ƙurmus yayin da motocin haya guda biyu su ka yi karo a kan babban titin Kano-Kaduna a jiya Litinin.
Mutane huɗu kuma sun samu muggan raunuka a haɗarin  da ya faru a garin Tsamawa da ke Ƙaramar Hukumar Garun Mallam ta Jihar Kano da misalin ƙarfe 3 na yamma.
Kakakin Hukumar Kwana-kwana ta Jihar Kano, Saminu Yusuf ya tabbatar da faruwar haɗarin.
Ya ce Hukumar, a reshen ta na Ƙaramar Hukumar Kura ta samu rahoton haɗarin da ga wani mai suna Isa Mai fetur.
Ya ce jami’an hukumar na zuwa wajen su ka tarar motocin tuni sun ƙone ƙurmus har ba a gane lambobin motocin su ba.
Ya ce mutane 12 sun ƙone ƙurmus har ba za a iya gane sunayen su da shekarun su ba, inda ya ƙara da cewa tuni a ajiye su a asibiti.