Home Labarai Fasto ya yi garkuwa da kansa sau biyu ya kuma karbi kuɗin fansa a Plateau

Fasto ya yi garkuwa da kansa sau biyu ya kuma karbi kuɗin fansa a Plateau

0
Fasto ya yi garkuwa da kansa sau biyu ya kuma karbi kuɗin fansa a Plateau

Rundunar ƴan sandan jihar Plateau ta cafke wani Fasto da ya yi garkuwa da kansa sau biyu tare da karbar kudin fansa a hannun masu bauta a cocinsa.

DSP Alfred Alabo, jami’in hulda da jama’a na rundunar ƴan sandan ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba a Jos.

Alabo ya ce ƴan sanda sun kama wanda ake zargin ne a watan Nuwambar 2022.

“Rundunar ƴan sanda ta bankado munanan aika-aikar da wani Fasto Albarka Sukuya da ke Jenta Apata, Jos ya aikata, wanda a lokuta da dama ya yi garkuwa da kansa da kansa, tare da abokan aikata laifi, har da karbar kudin fansa daga masu tausaya wa a masu bauta a cocin sa.

“Sakamakon haka, a ranar 14 ga watan Nuwamba da 15 ga Nuwamba, 2022, inda masu tausaya masa suka biya Naira 400,000 da kuma N200,000 a matsayin kudin fansa domin a sake shi, lamarin ya janyo zargin cewa ƙarya ne.

“Ta hanyar sahihan bayanan sirri, DPO na ofishin ƴan sanda na Nasarawa Gwong, CSP Musa Hassan ya gayyaci malamin kuma aka fara bincike nan take.

“A binciken da ake yi, an gano cewa wanda ake zargin yana hada baki da ‘yan kungiyarsa wajen yin garkuwa da shi da kuma karbar kudin fansa da zamba. Ya amsa laifin aikata laifin,” inji shi.

Mista Alabo ya ce wanda ake zargin ya bayyana sunayen wasu ’yan kungiyarsa uku, inda ya ce an kama biyu daga cikinsu yayin da daya kuma ya tsere.