Home Labarai Fasto ya roki kotu da ta raba aurensa bisa zargin matarsa da saka shi neman mata

Fasto ya roki kotu da ta raba aurensa bisa zargin matarsa da saka shi neman mata

0
Fasto ya roki kotu da ta raba aurensa bisa zargin matarsa da saka shi neman mata

Hassan Y. A. Malik

Wani Fasto dan shekaru 41, mai suna Oluwasanjo Eniola, ya rankaya kotu a garin Ibadan ta jihar Oyo, inda ya roki kotun da ta raba aurensa da mai dakinsa, Basirat, da ya ce ta ki aminta da kiran da ubangiji ya yi masa na ya zama fasto da dai sauran zarge-zarge da ya gabatar a gaban kotun.

Fasto Oluwasanjo, ya kara da cewa rashin kulawar da baya samu daga matarsa, Basirat ya jefa shi harkar mu’amala da mata, inda har tsautsayi ya sanya ya samu dan gaba da fatiha daga wata mabiyiyarsa ta coci

Ya ci gaba da bayyana matarsa a matsayin wacce bata agaza masa wajen ciyar da cocinsa gaba saboda bata aminta da kasancewarsa Fasto ba, a maimakon haka ma sai ta dai ta tsangwame ni da korafe-korafe na babu gaira babu dalili.

A wani lokaci ma sai da ta bar gidanmu na aure ta koma jihar Legas da zama, kuma ta yi hakan ne ba tare da izini na ba.

Wannan ya jefa ni cikin halin kadaici, dalilin da ya sanya na fara kawance da daya daga cikin matan da ke cocina kuma har haka ya kaimu ga tarawa wanda daga karshe ta samu juna biyu, na buge da samun da a wajen aure.

A nata bayanin, Basirat mai shekaru 34, ta roki kotu da ta taimaka kar ta raba aurenta da mijinta na kusa shekaru 24.

Basirat ta ce, a tsawon shekarun da muka yi tare na haifa masa ‘ya’ya 4, saboda haka in an raba aurenmu, babu namijin da zai aure ni bayan na haifi ‘ya’ya 4 a wani gidan.

Ta kuma zargi mijin nata da haddasa duk wani rikici da ke tasowa a gidan nasu, inda ta fadawa kotu cewa, korafinta na da nasaba ne da neman matan cocinsa da ya ke yi wanda hakan har ya kai shi ga dirkawa wa wata ciki wacce ta haifa masa da.

Kuma ko tafiyar da na yi zuwa jihar Legas, da izininsa na tafi. Shi ya bani izini na je na yi aikatau a lokacin muna cikin halin babu.

“A saboda haka ina rokon wannan kotu da ta bamu dama mu sulhunta. Na dauki alkawarin za ba shi duk hadin kan da ya ke da bukata in har muka yi sulhu.” inji Basirat

Mai shari’a Ramoh Olafenwa ya daga sauraren karar zuwa ranar 28 ga watan Fabrairu, 2018 don bawa ma’auratan damar su je su yi sulhu. Ya kuma roki ma’auratan da su bawa sulhu da zaman lafiya dama.