Home Labarai Fati Slow ta shiga cacar bakin Naziru Sarkin Waka da Nafisa Abdullahi

Fati Slow ta shiga cacar bakin Naziru Sarkin Waka da Nafisa Abdullahi

0
Fati Slow ta shiga cacar bakin Naziru Sarkin Waka da Nafisa Abdullahi

 

Tsohuwar jarumar Kannywood, Fati Usman da a ka fi sani da Fati Slow ta fito ta goyi bayan caccakar abokiyar sana’arta, Nafisa Abdullahi da Naziru Ahmad ya yi kan zagin iyayen da ke tura ƴaƴansu almajiranci.

Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a makon da ya gabata ne dai Nafisa ta wallafa a shafinta na twitter, inda ta caccaki iyayen da ke tura ƴaƴansu almajiranci.

Bayan ta yi wannan furuci ne, sai Naziru Ahmad, wanda a ka fi sani da Sarkin waƙa, ya mayar mata da martani, lamarin da ya haifar da cecekuce tsakanin su.

Sai dai kuma Fati Slow sai ta shigar wa Naziru, inda ta yi wani faifen bidiyo ta na gaggaya wa Nafisa maganganu a fakaice.

Fati Slow ta ce tabbass babu asararre sama da mutumin da zai dunga iskanci yana watsawa duniya ana zagin iyayensa amma ko a jikinsa .

Tsohuwar jarumar ta bayyana cewa sai inda karfinsu wajen fada ma duk mutumin da zai zagi almajirai gaskiya.

A wani bidiyo da ta saki a shafinta na Instagram inda a ciki ne ta yi shagube ga Nafisa, ta bayyana cewa jarumar bata da ilimin addini shi yasa har take iya kalubalantar tura yara almajiranci domin su koyo ilimin addininsu.

“Naziru wannan maganarka gaskiya ne babu cikakken dan iska kuma wanda iyayensa ma basu san yadda za su yi da shi ba shine wanda zai yi iskanci ya turo duniya ana ta zagin iyayenshi yana dariya, shine cikakken dan iska.

“Kuma wanda yake ganin Naziru bai yi daidai ba, Naziru ya fito ya yi magana ka yi abun da za ka yi ko ki yi abun da za ki yi, ya fito nya fadi abun da ke ransa nima na fito na fadi abun da ke cikin raina.

“Ai cikakkiyar jahila ce ke, abun da yasa nace cikakkiyar jahila c eke ai baki da ilimin addini, muma ba shi garemu ba don haka baki isa ki ci mutuncin almajiri ba, baki isa ki zagi almajiri ba. Zagin almajiri ba daidai bane kuma sai mun yi magana saboda ba tsoron wani muke ji ba.”

Daily Nigerian Hausa ta tuna lokacin da ita ma Fati Slow ɗin ta gaggaya wa Nazirun magana a kan ya taɓa ƴan Kannywood, inda shi kuma a nasa martanin, sai ya bata kyautar Naira Miliyan ɗaya.