
Tsohon Gwamnan jihar Ekiti Peter Ayodele Fayose ya mika kansa ga hukumar EFCC a ranar talata kamar yadda yayi alkawarin cewar zai mika kansa ya hukumar don a bincike shi.
Fayose ya samu rakiyar Gwamnan jihar Ribas Nsome Wike da kuma tsohon ministar harkokin jiragen sama Femi Fani-Kayode da sauran ‘yan jam’iyyar PDP.