
Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta bayyana Gwamna Ahmadu Fintiri na jam’iyyar PDP a matsayin wanda ya lashe zaben gwamnan jihar.
A tuna cewa an sake zaben ne sakamakon ratar kuri’u da ƙuri’un da aka sossoke.
Alkaluman da aka sanar a ranar 20 ga watan Maris, Aishatu Binani ta jam’iyyar APC, ta samu kuri’u 390,275, yayin da Fintiri ya samu kuri’u 421,524.
Bayan sake zaben a ranar Asabar, an dakatar da tattara sakamakon zaben a ranar Lahadi, biyo bayan cece-kucen da aka yi kan ayyana Binani a matsayin wacce ta lashe zaben jihar.
Kwamishinan zabe, REC na jihar, Barr. Yunusa Ari ne yayi sanarwar ana tsaka da tattara sakamakon zaɓen na kananan hukumomi, lamarin da ya sanya aka dakatar da sanar da sakamakon.
Da ya ke bayyana sabon sakamakon da aka tattara a yau Talata, jami’in zaben, Farfesa Muhammed Mele, ya sanar da Fintiri a matsayin wanda ya lashe zaben.
A cewarsa, Finitiri, wanda shi ne gwamna mai ci, ya samu kuri’u 430,861 inda ya doke abokiyar karawar sa Binani ta jam’iyyar APC da ta samu kuri’u 396788.