
Allah Ya yi wa fitaccen ɗan wasan fina-finan Hausa, Sani Garba, wanda a ka fi sani da SK rasuwa.
Marigayin ya rasu a yau Laraba a birnin Kano, bayan ya sha fama da rashin lafiya.
Wani fitaccen mai shirya fina-finai, Abdul M. Amart ne ya tabbatar wa da BBC rasuwar ɗan jarumin.
Amart ya baiyana cewa marigayin ya rasu ne a Asibitin Muhammadu Abdullahi Wase da ke Kano a yau Laraba da yamma.
“Sani SK ya kai kusan shekara uku yana jinya a tsattsaye, amma rashin lafiyar ta taso masa sosai ne a baya-bayan nan inda ya shafe mako biyar yana jinya a asibitin,” in ji Amart.
Amart ya ƙara da cewa tun asali cutar ciwon suga ce yake fama da ita, wacce daga bisani ta haifar masa da cututtuka irinsu ƙoda da hanta da hawan jini.
A baya dai an sha yaɗa jita-jitar rasuwar Sani SK, inda ya dinga musantawa da kansa ma a wasu lokutan.
“A ranar yau da ya rasu ɗinnan aka fara yi masa wankin ƙoda,” a cewar Amart, wanda shi ke tsaye a kan kula ɗaukar nauyin kula da lafiyar marigayin.
Sani Garba SK ɗan asalin unguwar Zage ne a cikin birnin Kano, kuma a baya kafin ya fara harkar fina-finai mai waƙoƙin begen Manzon Allah ne a ƙungiyar Usha’un Nabiyyu.
Daily Nigerian Hausa ta jiyo cewa a gobe Alhamis ne dai za a yi jana’izar mamacin a gidansa da ke Mandawari.