Home Kanun Labarai Fursunoni 36 masu matuƙar hatsari sun arce daga kurkuku

Fursunoni 36 masu matuƙar hatsari sun arce daga kurkuku

0
Fursunoni 36 masu matuƙar hatsari sun arce daga kurkuku

A ƙalla ‘yan kurkuku 36 ne suka arce daga gidan yarin Ikot Ekpene dake jihar Akwa-Ibom, bayan wasu ‘yan kurkukun sun samu nasarar kutsa kai  ɗakin dafa abincin kurkukun, kuma suka dauki wukake,inda suka farwa ma’aikatan da sara.

A wata sanarwar da kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Obgajie Ogbajie ya fitar, yace jami’an ‘yan sandan su sun ci nasarar harbin mutum 4 daga cikin mutanen da suka yi nufin tserewa.

Haka kuma, Ogbajie yace, anci nasarar damke mutum 7 daga cikin waɗan da suka tsere nan take.

“Da misalin karfe 1147 na daren ranar Laraba, 27 ga watan Disambar 2017  ɗinnan, ankaiwa wasu masu aikin dafa abincin gidan yarin hari, wanda wasu fursunoni dake gidan yarin na Ikot Ekpene suka kai musu”

“Sun ci nasarar kwace wata kakkaifar wuka daga hannun daya daga cikinmasu aikin dafa abincin gidan yarin, sannan yayi mata wani mugun yanka, inda daga nan ne ya baiwa sauran ‘yan kurkukun dammar shigowa inda ake dafa abincin domin su kwashi sauran wukake, sannan suka ci nasarar fatattakar ma’aikatan dafa abincin”

“Bayan an kwashi lokaci ana batarnaka, an harbi mutum 4 daga cikin ‘yan kurkukun inda nan take suka mutu, sannan kuma, aka ci nasarar cafke mutum 7, yayinda mutum 36 suka ci nasarar tserewa, amma jami’an tsaro tuni suka kaddamar da wani bincike na musamman domin gano inda suka boye”

“Bayan haka kuma, Babban jami’in da ke kula da rundunar kula da ‘yan kurkuku ta kasa reshen jihar ta Akwa-Ibom, Alex Oditah ya bayar da umarnin a gudanar da binciken musabbabin faruwar wannan al’amari da ked a ban takaici”

“Haka shima, Kwamishinan ‘yan sandan jihar ya bukaci al’umma das u kwantar da hankalinsu, kuma su taimakawa da jami’an tsaro da dukkan wasu bayanai da zasu kai ga cafke wadan da suka ci nasarar sulalewa daga gidan kurkukun,  sannan kuma ya tabbatarwa da al’umma cewar, an tsaurara matakan tsaro a dukkan gidajen kurkukun dake fadin jihar domin kare sake aukuwar hakan nan gaba”.