
Wani fusataccen mai goyon bayan ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Everton ya jefo wa ɗan wasan gaban ƙungiyar, kuma ɗan asalin Nijeriya, Alex Iwobi, rigar da ya bashi bayan an tashi daga wasa.
A jiya Asabar ne dai Everton, wacce ta yi tattaki zuwa gidan Bournemouth ta sha kashi 3-0.
Kwallayen da Marcus Tavernier da Kieffer Moore da Jaidon Anthony suka ci sun ishe Everton rashin nasara, wasan da ya fusata magoya Everton ɗin da su ka biya kuɗin mota har zuwa Bournemouth amma kungiyarsu ta sha kashi.
Hakan ne ya sanya bayan an busa tashi, bayan da ƴan was Everton ɗin su ka zo wajen magoya bayansu domin su yi musu jinjina, sai shi Iwobi ya jefa wa wani mai goyon Everton rigar sa kyauta, amma sai ya jefo wa Iwobin kayar sa.
Kocin ƙungiyar, Frank Lampard ya goyi bayan abinda mai goyon bayan Everton ɗin ya yi, inda ya ce “magoya bayan mu na da ƴancin su ji bakin ciki idan a ka ci mu a wasa, sabo da haka ni ban ga laifin su ba,”in ji Lampard