
Wasu fusatattun matasa sun bankawa Noble Kids Academy wuta da ke Kwanar Dakata a Jihar Kano.
Makarantar ita ce ta Abdulmalik Tanko, wanda ya yi garkuwa da wata yarinya dalibarsa, Hanifah Abubakar, sannan ya yi mata kisan gilla.
Tuni dai jami’an tsaro su ka cafke Tanko yayin da ya ke shirin karɓar kuɗin fansa.
Tun da fari dai Gwamnatin Jihar Kano ta bada umarnin rufe makarantar, sannan ta karɓe lasisin gudanar da ita.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa tun lokacin da a ka kama Tanko, fusatattun matasan ke yunƙurin ƙone makarantar, amma rahotanni sun yi nuni da cewa dangin Hanifah ɗin ne su ka hana sabo da ginin ba na shi ba ne, na haya ne.
Amma duk da haka, sai matasan su ka biyo tsakar dare su ka cinnawa ginin wuta domin nuna fushin su a kan kisan gillar da a ka yi wa Hanifah.
Tuni dai kisan na Hanifah ya ja hankalin duniya, inda Shugaban Ƙasa Muhammadu Buhari, Gwamna Abdullahi Ganduje, ƴan siyasa da sauran ƙungiyoyi ke kira da a bi wa iyayen Hanifah haƙƙin marigayiyar.