Home Labarai An gama jigilar kwashe fasinjojin da harin ƴan ta’adda kan jirgin ƙasan Abuja-Kaduna ya rutsa da su

An gama jigilar kwashe fasinjojin da harin ƴan ta’adda kan jirgin ƙasan Abuja-Kaduna ya rutsa da su

0
An gama jigilar kwashe fasinjojin da harin ƴan ta’adda kan jirgin ƙasan Abuja-Kaduna ya rutsa da su

 

A safiyar yau ne jami’an tsaro da jami’an Hukumar Bada Agajin Gaggawa ta Jihar Kaduna, SEMA da kuma ƙungiyar agaji ta Red Cross ta Nijeriya su ka kammala kwashe fasinjojin da su ka maƙale a cikin jirgin ƙasan Abuja-Kaduna da ƴan ta’adda su ka kai wa hari a yammacin jiya Litinin.

Sanarwar da Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin Gida na Kaduna, Samuel Aruwan ya fitar ta ce, an kai fasinjojin da suka samu raunuka, da wasu da suka jikkata zuwa asibiti.

“An kwashe fasinjojin daga wurare daban-daban masu wuyar shiga a cikin dazuzzuka da duwatsu a cikin Audujongom, kusa da hanyar Kaduna zuwa Abuja.

“Kamar yadda aka bayyana a jiya, gwamnatin jihar Kaduna na ci gaba da tuntubar hukumar kula da jiragen kasa ta Najeriya (NRC) don tantance fasinjojin da ke jirgin,” in ji Mista Aruwan.

Gwamna Nasir El-Rufa’i, wanda ya yabawa duk wadanda su ka bada gudunmawa wajen kwashe fasinjojin da su ka samu raunuka, ya yi kira ga asibitocin da su kula da marasa lafiyan yadda ya dace.

Gwamnan ya kuma umurci ma’aikatar lafiya da ta tuntubi asibitocin domin gwamnati za ta dauki nauyin kula da lafiyarsu.