
Shugaban Jam’iyyar APC na Ƙasa, Abdullahi Umar Ganduje ya roƙi gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf da ya fice daga jam’iyyar NNPP mai mulki a jihar ya dawo APC.
Ganduje ya baiyana hakan ne a wajen taron masu ruwa da tsaki na APC da aka gudanar a jihar Kano a yau Alhamis.
A cewar sa, a karshen taron, an yanke shawarar janyo ƴan sauran jam’iyyu zuwa APC domin a mayar da Kano ta zama jihar APC kaɗai.
Ganduje ya tabbatar wa gwamna Abba cewa idan ya shigo APC, zai samu kwanciyar hankali da zaman lafiya.
Ya ce tuni jam’iyyar a matakin kasa ke tuntuba da tattaunawa da ƴan sauran jam’iyyu da nufin dawowa APC, inda ya bayyana cewa yanzu haka wasu gwamnoni na daf da sauya sheka zuwa jam’iyyar mai mulki a kasa.