
Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya kalubalanci dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar NNPP Rabi’u Musa Kwankwaso da shi ma ya gudanar da taro a Kano domin gwada farin jininsa.
Ganduje ya bayar da wannan kalubalen ne a wata hira da ya yi da gidan talabijin na Channels TV, a shirin Politics Today a jiya Litinin.
Ganduje, ya kare ɗumbin magoya bayan dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar sa, Bola Tinubu a jihar a wani taro da aka gudanar a ranar Lahadi.
“Kwankwaso dan takarar shugaban kasa ne, ko shakka babu. To mu ma muna nan da ƙarfin mu kuma da yawa daga cikin mutanensa suna cikin jam’iyyarmu,” inji shi.
“Don haka, idan Kwankwaso ya na tunanin zai iya lashe zaɓe a jam’iyyarsa, to ya ya shirya tattaki irin wannan, ya ga abin da zai faru idan zai iya