Home Siyasa Ganduje ya amince wa jam’iyyu su yi amfani da filayen taruka don yin kamfe a Kano

Ganduje ya amince wa jam’iyyu su yi amfani da filayen taruka don yin kamfe a Kano

0
Ganduje ya amince wa jam’iyyu su yi amfani da filayen taruka don yin kamfe a Kano

Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Ganduje, ya bayar da umarnin a buɗe filin wasan ƙwallon ƙafa na Sani Abacha da sauran filayen gwamnati ga dukkanin jam’iyyun siyasa domin yakin neman zabensu na zaɓen 2023.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kwamishinan yaɗa labarai na jihar, Muhammad Garba, ya fitar a jiya Litinin a Kano.

Malam Garba ya ce hakan ya biyo bayan kudirin gwamnati na ganin an samar da daidaito ga dukkanin jam’iyyun siyasar jihar.

“Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) mai mulki a jihar Kano ta yi imanin cewa a matsayin su na ƴan kasa, jam’iyyun adawa ma na da hakkin yin amfani da kayan gwamnati wajen gudanar da yakin neman zabe,” inji shi.

Sai dai kuma Garba, wanda shi ne mai magana da yawun kungiyar yakin neman zaben Gawuna/Garo, ya ce duk da haka, dole ne sai jami’an tsaro sun baiwa jam’iyyunnnizini kafin a ba su damar shiga irin wadannan wurare kamar filin wasa.

Ya ce gwamnatin jihar ta tsaya tsayin daka kan manufofinta na ba da hakki daidai a matsayin alamar mutunta manufofinta na dimokuradiyya.

Malam Garba ya kuma bayyana fatan jam’iyyun za su gudanar da yakin neman zabensu cikin lumana.