
Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya yi kira ga ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau da su dawo su ci gaba da tafiya domin ƙara ƙarfafa Jam’iya mai mulki ta APC a jihar.
A jiya Alhamis ne dai Kotun Ɗaukaka Ƙara da ke Abuja ta shure hukuncin da Babbar Kotu a Abuja ta yanke, inda ta tabbatar da zaɓen shugabannin jami’ya na jiha ga ɓangaren Sanata Ibrahim Shekarau a Jihar Kano.
Bayan da ta tabbatar da dukka ƙararraki ukun da ɓangaren Ganduje ya shigar, Kotun Ɗaukaka Ƙarar ta ce babbar kotun da ta yanke hukuncin baya ba ta da hurumin yin hakan.
Kotun ta ƙara da cewa shari’ar ba a kan lamarin da ya faru kafin zaɓe ba ne, kawai dai rikici ne na cikin jam’iyya.
Da ya ke kaiwa Shugaban Riƙon Ƙwarya na APC na Ƙasa, Mai Maka Buni ziyarar godiya a Abuja a jiya, Ganduje ya ce kashi 100 bisa 100 a Kano APC a ke yi.
A cewar Ganduje, dukka ɓangarori biyun da ke rikici a APC su ke, inda ya yi kira gare su da su dawo a ci gaba da tafiya domin ci gaban jam’iyar.
Gwamnan ya kuma tabbatar da cewa tuni dai shelkwatar jam’iya ta ƙasa ta mika wa Abdullahi Abbas takardar shaidar zama sahihin shugaban jam’iyya na jiha.
Ya kuma gode wa Ubangiji da duk sauran ƴan jamiyya da su ka bada goyon baya a lokacin shari’ar.