Home Labarai Ganduje ya baiwa Dangote, Abdussamad, Dantata muƙami

Ganduje ya baiwa Dangote, Abdussamad, Dantata muƙami

0
Ganduje ya baiwa Dangote, Abdussamad, Dantata muƙami

 

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya naɗa Aliko Dangote, Aminu Dantata da Abdussamad Isyaku Rabiu a matsayin mambobi na kwamitin gudanarwa na Hukumar Zakka da Hubusi ta Kano.

Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Muhammad Garba ne ya baiyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a yau Laraba.

Garba ya ce Dakta Ibrahim Muazzam Maibushira, shi ne a ka naɗa a matsayin Shugaban kwamitin.

Sauran, a cewar Kwamishinan, sun haɗa da Dakta AbdulMutallab Ahmed a matsayin Kwamishina I sai kuma Dakta Lawi Sheikh Atiq a matsayin Kwamishina na ll a hukumar.

Sauran sun haɗa da wakilan Masarautar Kano, wakilan Ma’aikatar Yaɗa Labarai, Wakilan Ma’aikatar Harkokin Addinai, sai na kasuwannin kurmi, Rimi, Kwari da Singa.