Home Labarai Ganduje ya bar wa Kano bashin Naira biliyan 241.5, Abba Gida-Gida ya nuna takaici

Ganduje ya bar wa Kano bashin Naira biliyan 241.5, Abba Gida-Gida ya nuna takaici

0
Ganduje ya bar wa Kano bashin Naira biliyan 241.5, Abba Gida-Gida ya nuna takaici

Sabon Gwamnan Jihar Kano, Injiniya Abba Kabir Yusuf ya bayyana takaicin yadda tsohon gwamnan jihar, Abdullahi Umar Ganduje ya bar wa jihar ɗumbin bashi, har Naira biliyan 241.5.

Abba Gida-Gida ya nuna takaici ne a yayin bikin karɓar mulki, wanda ya gudana a Ante-chamber da ke cikin gidan gwamnatin jihar.

Sai dai kuma Ganduje bai halasci wajen miƙa mulkin ba, inda wannan shi ne karo na farko da aka yi karɓar mulki bangare da gwamna mai mika mulki ba a tarihin jihar Kano.

Da ya ke magana yayin mika mulkin, tsohon sakataren gwamnatin jihar, Alhaji Usman Alhaji, wanda ya wakilci Ganduje, ya ce gwamnatinsu ta bar bashin Naira biliyan 241.5.

Sai dai kuma wannan bayani bai yi wa Abba daɗi ba inda ya bayyana cewa wannan makudan kudaden sun zamo nauyi a kan gwamnatin, inda ya ce” ina zan samo kuɗin da zan biya wannan bashin?

“Dole nanfadinhaka sabo da al’ummar Kano su san me ake ciki. Kuɗin da ake tarawa, da wanda ake tarawa na haraji duk suna ina?,in ji shi.

Abba ya kuma ci alwashin sai ya binciki wannan makudan kudade da Ganduje ya bar wa gwamnatin Kano.