
Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya tafi Ƙasar Amurka domin ɗaukar wani kwas na mako ɗaya a jami’ar Havard.
Wata sanarwa da Kwamishinan Yaɗa Labarai, Muhammad Garba ya fitar ta ce gwamnan ya tafi ne domin yin wani kwas mai taken “Sahihiyar hanyar bunƙasa harkar mulki” a makarantar koyon harkar kasuwanci ta jami’ar Havard da ke Boston.
Sanarwar ta ce Ganduje ya danƙa ragamar mulki da cikakken iko ga mataimakinsa, Nasiru Gawuna a matsayin gwamnan riƙon-ƙwarya.
Sanarwar ta ƙara da cewa, gwamnan ya bada umarnin cewa duk wata hada-hadar kuɗi a kaiwa ofishin mataimakin gwamnan domin yin abinda ya dace.