
An hango Gwamnan Kano Abdullahi Umar Ganduje a wani faifan bidiyo da aka dauka bai sani ba yana karbar cin hancin dalar Amurka miliyan biyar.
Tuni dai hukumomin tsaro suka dukufa inda aka samo kwararru domin tantance sahihancin wannan bidiyo domin daukar hukunci kan abin.
Bayanai sun tabbatar da cewar an kaiwa Shugaban kasa wannan faifan bidiyo don ganewa idonsa.