
A yau Laraba ne dai Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje ya maye gurbin Ciyaman ɗin Kungiyar Ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars, Surajo Shuaibu Yahaya, da shugaban Hukumar Wasanni ta Jihar Kano, Ibrahim Galadima.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa a ranar Asabar ne Hukumar Shirya Gasar Firimiya ta Ƙasa, LMC ta kori tsohon Ciyaman ɗin na Kano Pillars, Suraj Yahaya, wanda a ka fi sani da Jambul daga ƙungiyar.
LMC ta ce korar Ciyaman ɗin ta biyo bayan laifin cin zarafin mataimakin alƙalin wasa.
A wata sanarwa da ya fitar ta hannun babban sakataren yaɗa labaransa, Abba Anwar, Ganduje ya ce “Kamar yadda kungiyar Kano Pillars ke kara fuskantar matsin lamba a gasar firimiya ta kasa, zai yi kyau a samu shugabancin da zai jagoranci ƙungiyar.”
“Ibrahim Galadima, shugaban hukumar wasanni ta jihar Kano, yanzu zai maye gurbin Ciyaman ɗin Kano Pillars FC na yanzu, Surajo Shu’aibu Yahaya, a matsayin muƙaddashi, kafin a naɗa Ciyaman na dindindin,” Gwamna Ganduje ya bayyana a cikin sanarwar.
Sanarwar ta ce nadin na nan take ne.