Home Labarai Ganduje ya sake naɗa Baffa Dan’agundi a matsayin shugaban CPC na riƙo

Ganduje ya sake naɗa Baffa Dan’agundi a matsayin shugaban CPC na riƙo

0
Ganduje ya sake naɗa Baffa Dan’agundi a matsayin shugaban CPC na riƙo

 

Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya amince da naɗin Shugaban Hukumar kula da Zirga-zirgar Ababen Hawa ta Kano, KAROTA, Baffa Babba Dan’agundi a matsayin Shugaban Hukumar Kare Hakkin mai Saye, CPC na riƙo.

Daily Nigerian Hausa ta tuna cewa Ganduje, a shekarar da ta gabata ya naɗa Dan’agundi a matsayin shugaban CPC din na riƙon ƙwarya kafin ya naɗa Idris Dambazau a matsayin shugaban hukumar na din-din-din.

A wannan karon ma, a wata sanarwa da Babban Sakataren Yada Labarai na Gwamna Ganduje, Abba Anwar ya fitar a yau.

Sanarwar ta ce naɗin na Dan’agundi ya fara aiki ne nan take, inda ya ce kuma an bashi damar kula da dukkanin al’amuran hukumar har zuwa lokacin da za’a naɗa Manajan Daraktar hukumar na din-din-din.