
Gwamnatin Jihar Kano ta sauya sunan Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Wudil, KUST zuwa Jami’ar Kimiyya da Fasaha ta Dangote, ADUST.
Daily Nigerian Hausa ta rawaito cewa majalisar zartaswar jihar Kano ce ta amince da sauya sunan .
Kwamishinan Yaɗa Labarai na jihar, Malam Muhammad Garba, wanda ya bayyana hakan a wata sanarwa a ranar Asabar, ya ce ci gaban ya biyo bayan shawarar da kwamitin da aka tura jami’ar ya bayar.
Ya bayyana cewa a yanzu za’a rika kiran makarantar da ‘Aliko Dangote University of Science and Technology (ADUST)’, Wudil.
Malam Garba ya kara da cewa an mika batun ga majalisar dokokin jihar domin nazarin dokokin da suka kafa jami’ar domin yin gyara.