
Gwamna Abdullahi Ganduje na Jihar Kano ya umarci duk masu riƙe da mukaman siyasa a gwamnatinsa da ke son tsayawa takara a zaben 2023 da su yi murabus.
A wata sanarwa da babban sakataren yada labaran sa, Abba Anwar, ya fitar a yau Lahadi, Ganduje ya ce an baiwa wadanda aka naɗa muƙamai wa’adin daga yanzu zuwa gobe Litinin, 18 ga watan Afrilu, da su miƙa takardar murabus ɗin su.
Ya ce umarnin wani mataki ne na biyayya ga tanadin sashe na 84(12) na sabuwar dokar zabe da aka yi wa kwaskwarima.
Tun da farko, kwamishinan albarkatun ruwa na Ganduje, Sadiq Wali, ya mika takardar murabus dinsa kuma ya sayi fom ɗin tsayawa takarar gwamna a jam’iyyar adawa ta PDP.
Sai dai gwamnan ya ƙi amince wa da murabus din Baffa Dan’agundi, Manajan-Darakta na Hukumar Kula da Zirga-zirgar Ababen hawa ta Kano, KAROTA.