
A jiya Laraba ne dai guda cikin masu neman tikitin takarar dan majalisar tarayya daga Ƙaramar Hukumar Birnin Kano, karkashin jam’iyyar NNPP, Yusuf Sharada, ya fice da ga jam’iyar, inda ya koma APC, ƙarƙashin Gwamna Abdullahi Umar Ganduje.
Daily Nigerian Hausa ta tattaro cewa a jiya da daddare ne dai Sharada ya ziyarci Gwamna Ganduje, jim kadan bayan fidda sunayen ƴan takarkaru da jam’iyyar NNPP tayi Jiya a jihar Kano, inda shi kuma babu sunansa.
Bayan gama ganawar su da Ganduje, sai Gwamnan ya cire wa Sharada jar hularsa tare da maye masa gurbinsa da wata.
Sharada dai yana cikin wadanda suka ci gajiyar tallafin karatu a zamanin mulkin tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.