Home Siyasa Ganduje ya ƙwato ɗan majalisa da Ciyaman da ga hannun NNPP

Ganduje ya ƙwato ɗan majalisa da Ciyaman da ga hannun NNPP

0
Ganduje ya ƙwato ɗan majalisa da Ciyaman da ga hannun NNPP

 

 

Bayan da Murtala Musa Kore, ɗan Majalisar Jiha mai Wakiltar Mazaɓar Ƙaramar Hukumar Dambatta da Mohammed Abdullahi Kore, Shugaban Ƙaramar Hukumar Dambatta su ka sauya sheƙa daga APC zuwa NNPP, ƴan siyasar sun yi mi’ara-koma-baya a kan matakin da su ka ɗauka.

A ranar Alhamis ne dai Kore da Kore su ka bi Shugaban Ma’aikatan Fadar Gwamnan Jihar Kano, Ali Haruna Makoda zuwa NNPP, bayan ya ajiye aikinsa ya kuma sauya sheƙa da ga APC.

Amma kuma a wani yanayi na yin amai a lashe, sai a ka jiyo Kore da Kore, wasu faya-fayen radio da a ka riƙa yaɗa wa ta WhatsApp a jiya Lahadi, su na barranta kansu da koma wa NNPP mai alamar kayan marmari.

A cewar su biyun, abinda ya faru a ranar Alhamis ɗin wata ƴar matsala ce da ta sanya su ka yi saurin yanke hukunci, inda su ka kara da cewa daga baya sai su ka gano sun tafka kuskure.

Sun ƙara da cewa yanzu dai komai ya wuce kuma sun dawo APC, inda su ka jaddada goyon baya ga Gwamna Abdullahi Umar Ganduje da kuma yin mubaya’a da ɗan takarar gwamna, Nasiru Yusuf Gawuna da mataimakin sa, Murtala Sule Garo.

Kore da Kore sun kuma jaddada bukatar su ta taka gagarumar rawa wajen ganin APC ta samu nasara a duk matakan mulki a zaɓukan 2023.