
Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje,ya bukaci ‘yan Najeriya da su guji rikicin addini da na Siyasa a rungumi juna a zauna lafiya da juna.
Gwamna Ganduje yayi wannan kiran ne a ranar Asabar a taron hadin kai da fahimtar juna karo na biyu tsakanin al’ummomin da suke zaune a jihar Kano.
Kamfanin dillancin labarai na Najeriya NAN, ya ruwaito cewar, taron wanda Shugabannin kungiyoyin addinin Kirista da na Musulmi suka halarta a jihar Kano.
Haka kuma, Gwamnan ya kuma nemi a zauna lafiya, tare da rungumar juna wajen cudanya ba tare da cutarwa ko zalintar wani ba.
“Zaman lafiya zai samu ne, idan Shugabannin kungiyoyin addinin Musulunci da na Kirista suka rungumi kalamai na mutunta juna da zaman lafiya”
“Sai da zaman lafiya al’umma take iya samun cigaba”
“A sabida haka, nake kira ga dukkan bangarorin al’umma da su baiwa Gwamnati cikakken hadin kai da goyon baya, domin samun nasarar zaman lafiya a jihar Kano”
Bayan haka, Gwamna Ganduje yayi kira ga Malaman Addinin Musulunci da na Kiristanci da su yiwa mabiyansu wa’azi na a zauna lafiya da juna, domin samun zaman lafiya mai dorewa.
Sannan kuma, ya yabawa Shugaban kasa Muhammadu Buhari akan kokarinsa na yakar ‘yan ta’adda da kuma cin hanci da rashawa a Najeriya.
Sabon Shugaban kungiyar Kiristoci ta kasa CAN, reshen jihar Kano, Samuel Adeyemo, yayi kira da a fahimci juna tsakanin Musulmi da Kirista.
Mista Adeyemo ya kara da cewar, shirya irin wannan taro dama ce da za’a hadu domin tattauna batun zaman lafiya tsakanin mabiya addinin Musulunci da na Kiristanci.
Haka kuma, ya jinjinawa Gwamna Ganduje akan kokarinsa na ganin an samu fahimtar juna tsakanin Musulmi da Kirista a jihar Kano.
“Dole ‘yan Najeriya su rungumi zaman lafiya, ba tare da nuna bambancin addini ko yare ko kabila ba, sannan a guji kalaman da zasu jawo hautsini da cecekuce”
Shugaban Hukumar Hisba ta jihar Kano, Bashir Usman, yayi kiran da a dinga gudanar da irin wannan taron domin tattaunawa domin samun mafitar wasu abubuwa da aka samu rashin fahimta akansu.
Bashir Usman, ya bukaci al’ummar Musulmi da Kirista su dinga yin kira da a zauna lafiya a fahimci juna.
Sannan, ya yabawa Gwamna Ganduje a kokarinsa na ganin ya hada kan al’umma waje daya tsakanin Musulmi da Kirista a jihar Kano ba tare da nuna bambanci ba.
A lokacin da yake tofa albarkacin bakinsa a wajen, Mai Martaba Sarkin Kano, Muhammadu Sunusi, yayi kira da a samu fahimtar juna tsakanin Musulmi da Kirista a Najeriya. Sarkin wanda Makaman Kano, Sarki Ibrahim ya wakilta.
NAN