
Jami’ar Jihar Legas, LASU, ta baiwa Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje da na Jihar Borno, Babagana Umara Zulum digirin girmamawa.
Shugaban Jami’ar, Farfesa Ibiyemi Olatunji-Bello je ya sanar da bada kyautar digirin a yayin lakcar bikin yaye ɗalibai karo na 25 da jami’ar ta yi a yau Alhamis.
Sauran wadanda su ka karbi digirin girmamawar sun haɗa da Goodie Ibru, mamallakin Sheraton Lagos Hotel Plc; Abike Dabiri-Erewa, Shugabar Hukumar kula da Ƴan Nijeriya a Ƙasashen Waje, NiDCOM da kuma Ibukun Awosika, Shugaban banmin First Bank na Nijeriya.
Ya ce wadanda su ka karbi kyautar digirin an zaɓe su ne cikin tarin ƴan takara da dama, inda ya ƙara da cewa hakan ya nuna cewa sun yi zarra wajen gaskiya, sadaukarwa da kuma bada gudunmawa wajen hidimta wa ƙasa.