Home Labarai An gano yara huɗu da su ka ɓata a Kano

An gano yara huɗu da su ka ɓata a Kano

0
An gano yara huɗu da su ka ɓata a Kano

 

Kwamitin da Gwamnatin Kano ta kafa don nemo yaran da su ka ɓace s Jihar Kano ya gano wasu yara huɗu kuma tuni a ka sada su da mahaifan su.

Sakataren Gwamnatin Kano, Alhaji Usman Alhaji ne ya karbi yaran a hukumance a ofishinsa a jiya Juma’a.

Yaran sun haɗa da Abdullahi Yahaya mai shekara 14, Umar Sani,12, Isma’ila Sabo, 12, da Isah Haruna mai shekara 13.

Shugaban kwamitin, Wada Umar Rano ne ya kai yaran, inda ya ce an gano su ne a Jihar Legas da taimakon Ƴan sandan farin kaya, wato DSS.

Ya ce da a ka gano yaran, sai a ka yi gwajin halittun su da na mutanen da su ke riƙe da su, sai kuwa sakamakon gwajin ya nuna ba mahifansu ba ne.

Ya ƙara da cewa tuni a ka gano iyayen uku da ga ciki, dayan kuma a na nan a na neman mahifansa.

Ya ce tuni a ka danƙa guda ukun a hannun mahaifansu, inda ya yaba wa Gwamnan Jihar Kano, Abdullahi Ganduje bisa jajircewarsa wajen gano yaran.

Daily Nigerian Hausa ta tuna cewa a 2019 ne dai rundunar yan sanda ta jihar Kano ta gano wasu yara 9 da a ka sace a ka kai su garuruwan kudu, inda ta yi zargin an sayar da su da canja musu addini, lamarin da ya haifar da cecekuce a kasa baki ɗaya.

Hakazalika iyayen yara na fadin cewa yanzu haka a kwai yara sama da 100 da ba a gan su ba.