
Gwamnatin Jihar Kaduna ta saki wata sanarwa ta gargaɗi mai matuƙar muhimmanci ga mazauna jihar a kan shirin da ƴan ta’adda su ke na sanya bamabamai a cikin al’umma.
Gawantin ta sanar da hakan ne ta bakin Kwamishinan Tsaro da Harkokin Cikin gida a jiya Litinin.
Gwamnatin ta ce sanarwar ta zo ke bayan da jami’an tsaro su ka yi nazari akan yiwuwar ƴan ta’adda za su illata al’umma ta hanyar saka bamabamai a guraren al’umma kamar su asibitoci, otal-otal, makarantu, mashaya, guraren nishaɗi, guraren ibada da cin abinci da sauran su.
Sanarwar ta tabbatar da cewa jami’an tsaro na iya bakin ƙoƙari don tabbatar da cewa an kare al’umma da gine-gine a faɗin jihar.
Sanarwar ta kuma yi kira ga al’umma da su kai rahoton wani ko wani abu da ba a gamsu da shi zuwa hukumar tsaro mafi kusa.