
Daga Hassan AbdulMalik
Rundunar ‘yan sandan jihar Borno, a jiya Alhamis, ta yi gargadi ga mazauna babban birnin jihar, da su sanya idanu kan yadda abubuwa ke gudana a kusa da su, domin hukumar ta samu wani rahoton sirri da ke nuna cewa mayakan Boko Haram za su kai harin kunar bakin wake a wasu wurare da ba a tantance ba a Maiduguri da kewaye.
Mataimakin kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ahmad Bello ne ya bayyana hakan a wata sanarwa da ya fitar a Maiduguri, inda ya ce, ‘yan kunar bakin wake zai su hari inda akwai gungun mutane don aiwatar da mummunar akidarsu.
“Rundunar ‘yan sanda ta jihar Borno tare da hadin gwiwar rundunar soji ta Lafiya Dole na masu jan hankalin al’umma da su sanya idanu ga abubuwan da ke wakana a kewayensu, sakamakon rahoton tsaro da rundunonin suka samu na cewa Boko Haram ta yi shirin kaddamar da hare-haren bom a Maiduguri, kuma kungiyar ta Boko Haram za ta gabatar da hare-haren ne a wuraren taron mutane don ta samu halaka mutane da yawa ta hanyar yin amfani da motoci dauke da boma-bomai.
“Sakamakon wannan shiri na Boko Haram ne, ya sanya jami’an tsaro daga nasu bangaren suka dauki matakan kare wannan aikin ta’adanci da Boko Haram ke kokarin yi”
“Rundunar tsaron na bukatar mutane da su gaggauta kai mata rahoton duk wani abu da zuciyarsu bata gamsu da shi ba da suka hada da motsin mutane, ababen hawa ko wasu na’urori.”
“Muna masu baku tabbacin cewa rahoton da wanda ya bayar da shi zai kasance mun suturta su don tsare rai da lafiyar wanda ya bayar da rahoton,” rundunar ta bayyana