
An yi garkuwa da Shugaban Caji-ofis ɗin ƴan sanda, DPO na Fugar, ASP Ibrahim Aliyu Ishaq.
An ɗauke Ishaq ne a yankin kogin Ise, a kan tsohuwar hanyar Auchi-Ekperi-Agenebode a Jihar Edo.
Jaridar PRNigeria ta samu bayanin cewa masu garkuwar sun tuntuɓi iyalin DPO ɗin domin kuɗin fansa.
ASP Ishaq, kafin a yi masa sauyin wajen aiki, shine DPO na Chaji-ofis ɗin Dakata da ke Jihar Kano