
Kungiyar likitoci masu neman kwarewa ta kasa ta umarci mambobinta da su koma bakin aiki a yau Litinin bayan yajin aikin gargadi na kwanaki 7 da suka yi bisa garkuwa da mambar su, Dakta Ganiyat Popoola.
An yi garkuwa da Popoola ne watanni 8 da su ka gabata kuma har yanzu ba a sako ta ba.
Koda ya ke, kungiyar ta ce zata sake yin duba kan kokarin gwamnatin tarayya na magance bukatar ta ta cikin makwanni 3.
A ranar Litinin din da ta gabata ne dai likitocin suka fara yajin aikin na gargadi domin matsawa don ganin an kubutar da likitar wacce ke kula da cibiyar kula da lafiyar ido ta Kaduna.
An sace ta da mijinta a ranar 27 ga watan Disamba na 2023.
Yayin da aka saki mijinta a watan Maris, Popoopla da dan uwanta sun kasance a hannun masu garkuwa da mutane.
Gwamnatin tarayya dai a ranar Alhamis ta ce zata dabbaka tsarin ‘Ba aiki ba biya’ ga likitocin.
Sai dai likitocin sun ce baza a yi musu barazana da hakan ba.
Da ya ke zantawa da jaridar Punch, shugaban kungiyar likitocin na kasa, Dakta Dele Abdullahi ya ce ” mun dakatar da yajin aikin a yanzu. Zamu gana domin ganin ci gaban da aka samu daga gwamnati nan da makwanni 3.”