
Wata majiya daga fadar SHugaban kasa ta tabbatarwa da cewar an garzaya da Yusuf Buhari zuwa kasar waje domin yin jinyarsa tare da duba lafiyarsa acan.
Bayanai na nuna cewar Yusuf Buhari ya samu karaya a hakarkarinsa da kuma buguwa akansa. Uwar gidan SHugaban kasa Aisha Buhari ta nuna godiyarta ga ‘yan Najeriya bias addu’o’I na fatan alheri da suke yiwa danta.
Mai Magana da yawun Shugaban kasa, Femi Adeshina yace Shugaba Buhari yana matukar godiya ga ‘yan Najeriya bias irin yadda suka dinga yin addu’o’I na fatan samun sauki ga Yusuf Buhari.