
A ci gaba da Gasar Firimiya ta England Arsenal ta lallasa Norwhich City da 5-0 a ranar da kocin ƙungiyar, Mikel Arteta ya cika shekara 2 cif-cif da karɓar ragamar ƙungiyar.
Bukayo Saka ne ya ci ƙwallaye 2, sai kuma Kieran Tierney, Alexandre Lacazette da Emile Smith Rowe kowa ya jefa ƙwallo ɗai-ɗai.