
Mai riƙe da kambun Gasar Firimiya ta Ƙasa, NPFL, Akwa United ta lallasa Kano Pillars 3-0 a gasar da a ka fara jiya Lahadi.
Pillars, wacce a ke yi wa laƙabi da Sai masu gida, ta sha kashi ne a gidan Akwa United a Uyo, babban birnin Jihar Akwa Ibom.
Ezekiel Bassey ne ya fara zura ƙwallo a ranar Pillars a minti na 45, a na daf da tafiya hutun rabin lokaci.
Jim kaɗan bayan an dawo daga hutun rabin lokaci, a daidai mintuna na 53 sai Stephen Chukwude shima ya jefa tashi ƙwallon.
A mintin ƙarshe na tashi da ga wasan ne kuma Ubong Friday ya rufe taro da addu’a, inda shima ya zura tashi ƙwallon da ta baiwa Akwa United nasar samun maki 3 da kuma ƙwallaye 3 a gasar ta bana.