
Yayin da a ke daf da fara kakar 2021-2022 ta gasar firimiya ta ƙasa, ƙungiyar ƙwallon ƙafa ta Kano Pillars ta shiga halin tsaka-mai-wuya, bayan da ta baiyana ƙarara cewa ba za ta riƙa yin wasannin gida a Kano ba.
Daily Nigerian Hausa ta tuno cewa, a watan da ya gabata ne dai Kamfanin da ke shirya Gasar Firimiya, LMC, ya kawo ziyara a filin wasa na Sani Abacha da ke Ƙofar Mata a Kano, inda ya gamsu da cewa Pillars, wacce a ke wa take da “Sai masu gida”, za ta yi wasannin ta na gida na kakar bana a ciki.
Kwamitin da ya zo duba filin wasan, ya baiyana cewa ƴan gyararraki kaɗan filin wasan ke buƙata, inda gwamnatin Kano ta tabbatar da cewa za ta yi gyaran.
Wannan jarida ta gano cewa a halin yanzu ma ana nan ana gyararraki a filin wasan na Sani Abacha, inda magoya bayan Pillars ɗin ke murna da cewa ƙungiyar za ta dawo yin wasannin ta na gida a Kano, bayan ta shafe kaka biyu ta na wasannin gida a filin wasa na Ahmadu Bello da ke Jihar Kaduna.
Ana cikin haka ne kuma, sai murna ta koma ciki, inda LMC ya yi amai ya lashe, bayan da ya baiyana cewa Pillars ba za ta yi wasannin firimiya ta bana ba har sai an sake ciyawar da a shimfiɗa a filin wasan, inda ya ce wacce ta ke kai yanzu ta tsufa.
A wata sanarwa da kakakin Pillars ɗin, Lurwanu Idris Malikawa ya fitar a ranar Talata, ya baiyana cewa LMC ɗin ta yi mi’ara-koma-baya a kan matakin ta na farko cewa Sai masu gida za su yi gasar bana a filin wasa na Sani Abacha.
Malikawa ya baiyana cewa Shugaban LMC, Malam Salihu Abubakar ya rubutowa ƙungiyar cewa ba za ta yi wasannin gida na kakar 2021-2022 ba har sai ta canja sabuwar ciyawa a filin.
“Mu muna nan muna jiran LMC ya sake aiko da kwamiti ya duba aikin gyararrakin da a ke yi a filin wasa na Sani Abacha domin ya bada tabbacin yin wasa na ƙarshe, abin mamaki, kawai sai mu ka ga sabuwar sanarwa daga LMC ɗin wai ba za a yi gasar firimiya ta bana a filin wasan mu ba har sai mun canja tsohuwar ciyawar filin mun shinfida sabuwa,”
Malikawa ya kuma baiyana cewa LMC ɗin ya umarci mahukunta Pillars da su zaɓi filin wasan da za su riƙa yin wasannin gida na gasar firimiya ta bana.