Home Wasanni Gasar Premier ta Ƙasa: Kano Pillars ta doke Katsina United 1-0

Gasar Premier ta Ƙasa: Kano Pillars ta doke Katsina United 1-0

0
Gasar Premier ta Ƙasa: Kano Pillars ta doke Katsina United 1-0

 

Kungiyar Kwallon Kafa ta Kano Pillars ta doke Katsina United da ci ɗaya mai ban haushi, 1-0, a fafatawar da su ka yi yau Alhamis a filin wasa na Moshood Kashamu Abiola dake Babban birnin tarayya Abuja.

Ɗan wasan Kano Pillars, Auwalu Ali Mallam ne ya zura Kwallon a ragar Katsina United a cikin mitunan ƙarin lokaci.

Idan za a iya tunatawa, an daga wasan ne bayan da hatsaniya da ta barke ana tsakiyar wasa tsakanin kungiyoyin biyu a filin wasa na Sani Abacha dake Kofar Mata a kwanakin baya.

Sai dai, a yau aka kammala wasan a filin wasa na Moshood Kashamu Abiola dake Babban birnin tarayya Abuja.

Hakan ya ba wa Kungiyar Kano Pillars damar darewa matsayi na goma sha shida acikin jerin kungiyoyi ashirin dake fafatawa a gasar ajin Kwarraru na Kasa.