Home Labarai Gasar Rubutu ta PSSG: Shiga nan ka ga ƙarin bayani kan yadda za a shiga gasar

Gasar Rubutu ta PSSG: Shiga nan ka ga ƙarin bayani kan yadda za a shiga gasar

0
Gasar Rubutu ta PSSG: Shiga nan ka ga ƙarin bayani kan yadda za a shiga gasar

PARLIAMENTARY SYSTEM SUPPORT GROUP (PSSG)

(Ɗan Asali)

KWAMITIN GASAR RUBUTU NA ƘASA na gayyatar masu sha’awar shiga gasar.

Taƙaitaccen Bayani: Kwamitin Gasar Rubutu na Kasa na gaiyatar haziƙan matasa a faɗin Nijeriya da su yi nazari na ilimi a kan makomar mulki a ƙasar nan.

An kirkiro wannan shiri ne domin duba yiwuwar sauyi daga tsarin mulkin da Nijeriya ke kai, na shugaba mai cikakken iko zuwa tsarin mulkin firaminista na usuli. Hakan na da nufin kimsa fahimta mai zurfi ga matasa akan tsarin dimokuraɗiyya da shugabanci na gari a Nijeriya.

Taken Rubutun: “Yayin da Nijeriya ke cika shekaru 25 a kan tsayaiyen tsarin mulkin dimokuraɗiyya, sai kuma ga wani batu ya ɓullo na cewa tsarin mulkin firaminista da ƙasar nan ta fara ya fi na shugaba mai cikakken iko da ake kai a yanzu. Ƴan gaba-gaba wajen rabon tabbatar da tsarin mulkin firaminista ɗin sun bada hujjar cewa tsari ne da babu wariya, ga wakilci ingantacce gami da gaskiya da rikon amana, inda dukkan waɗannan sune sinadaran da ke samar da tattalin arziki, cigaba da zaman lafiya mai ɗorewa.” Tattauna wannan batu.

Ranar karɓar rubutun: 12 ga watan Yuni (ƙarfe 12 na dare)

Ka’idojin Shiga Gasar:

i- Duk ɗalibai na makarantun gaba da sakandire za su iya shiga gasar a ko ina a faɗin duniya.

ii- Dole ɗan takara ya kasance ɗalibin da ya ke karatu a halin yanzu, ba wanda ya gama makaranta ba.

Tsarin Aiko da Rubutun:

i- Da turanci za a yi rubutun kuma a shafin “Word” na na’ura mai ƙwaƙwalwa za a yi.

ii- Kar rubutun ya haura ko ya yi ƙasa da kalmomi 2,000

iii- Rubutun ya kasance ƙirƙira ce ta marubuci ba kwafowa ya yi ba, domin za a saka a na’ura a tantance.

iv- A yi amfani da tsarin haruffa na “Times New Roman” mai girman 12, a kuma yi amfani da fadin sarari tsakanin layukan rubutu na 2.0.

Tsarin zaɓen ƴan takara:

i- Za a tantance rubutu ta hanyar duba kan ƙirƙira, maudu’in da ake magana a kai, zurfin bincike da kuma bin ƙa’idojin rubutu.

ii- Ƴan takarar da su ka kai ga zagayen ƙarshe na gasar, za a kira su su gabatar da rubutun na su a wani taro da za a shirya, inda za su kare rubutun nasu a gaban masu kallo da kuma alƙalai.

Kyaututtuka:

Za a bada kyautar kuɗaɗe ga ƴan takara 100 da da su ka shiga gasar.

Damar tallafin karatu da ɗaukar horo ga wasu zaɓaɓɓu da su ka samu nasara a gasar ƙarƙashin gwamnati da kungiyoyi masu zaman kan su da kuma samun damar yin rubuce-rubuce na musamman.

Za a kammala gasar da taron jin ra’ayoyin al’umma a ranar 1 ga watan Yuli ta hanyar gabatar da maƙaloli daga bakin wasu manyan mutane.

Za a tura rubutun da aka kammala zuwa ga http://www.pssg.ng

Domin karin bayani, a tuntuɓi kwamitin tsare-tsare ta:

Email: support@pssg.ng, parliamentarySSG@gmail.com

Lambar Waya: +234 (0)9013096849; +234 (0)8033977544