
2
Hukumar da ke kula da gasar Serie A ta ƙasar Italiya ta dakatar da kocin Ƙungiyar Ƙwallon Ƙafa ta AS Roma, Jose Mourinho wasanni biyu sakamakon faɗa wa alƙalin wasa, Luca Pairetto baƙar magana.
An sallami Mourinho ne a na daf da tashi da ga wasan da Roma ta yi kunne doki da Hellas Verona, bayan da a ka hango shi ya na yi wa alƙalin wasa masifa.
A na zargin cewa Mourinho, wanda har sai da mataimakin alƙalin wasa ya tare shi, ya faɗa wa alƙalin wasan cewa aiko shi a ka yi domin ya yi wa Roma fasha.
A cewar jaridar wasanni ta La Stampa, Mourinho ya kwalla da ƙarfi ya ce “dama an aiko ka ne da wani dalili, aiko ka a ka yi…,”