Home Nishaɗi Gasar tseren Raƙuma ta bana tayi armashi a Abu-Dhabi

Gasar tseren Raƙuma ta bana tayi armashi a Abu-Dhabi

0
Gasar tseren Raƙuma ta bana tayi armashi a Abu-Dhabi
Gasar tseren Raƙuma a birnin Abu-Dhabi

Gasar tseren Raƙumi abu ne da ba zaka taba iya raba shi da rayuwar mutanan birnin Abu-Dhabi ba. Wannan gasa na daya daga cikin wasanni mafiya muhimmanci da ake yi a birnin, domin hatta mutanen da ke zaune a wasu kasashen ‘yan asalin birnin kan koma gida domin shaida wannan gasa.

Wannan gasa, na jawo hankalin ‘yan yawo bude ido sosai suna tururwar zuwa birnin Abu-Dhabi domin ganewa idanunsu yadda wannan gasa ke gudana. Domin anan ne, zaka ga yadda ake yiwa Rakumi kirari yana takamako yana gudu.

Ita wannan gasa, tana da tarihi mai tsawo a birnin ABu-Dhabi dama yankin tsibirin larabawa gabaki daya. Domin wasa ne da ake yinsa, tun kusan shekaru fiye da 1000 a yankin Saharar gabas ta tsakiya, sai dai bikin yana shan bamban daga wani gari zuwa wani.

Kafin zamanantar da wasan Rakuman, a da can,Larabawa kan fita daji cikin Hamadar sahara, suna yin tsere a tsakaninsu da juna, da Rakumansu, suna haye ko basa haye. Abu ne da ba zaka taba raba shi da rayuwar Larabawa ba, musamman na Birnin ABu-Dhabi.

Sai dai gasar a bana ta kayatar matuƙa da gaske, ddomin kuwa baƙi daga sassa da dama na duniyar nan ne suka halarci wannan gasar da aka yi a Al-Wathba dake birnin na Abu-Dhabi. Gasar dai ana yin ta ne a ranakun Alhamis da Juma’ah a makon farko na Bazara.