
Gwamnan jihar Gombe, Muhammadu Yahaya, ya yabawa Munyal Kwairanga, bayan ta kafa tarihi a gasar matasa ta kasa karo na 8 da ke gudana a garin Asaba na jihar Delta, inda ta samu lambobin zinare har guda uku a wasannin tsalle-tsalle.
Munyal, wacce ta wakilci jihar Gombe a gasar, ta nuna kwarewa ta musamman a fannin motsa jiki da tsalle-tsalle, tare da tabbatar da kambu mafi kyau a kowanne fanni.
Yahaya, a cikin wata sanarwa da ya fitar a jiya Talata, mai dauke da sa hannun babban daraktan hulda da manema labarai na gidan gwamnatin Gombe, Ismaila Misilli, ya yabawa Munyal bisa hazakar da ta nuna, inda ya ce nasarar da ta samu ba wai kawai ta kara daukaka jihar Gombe ba ne, har ma ta nuna kwazon matasan jihar kan ayyukan da suka yi a matakin kasa.
Ya yi nuni da cewa, a bisa bajintar da ta yi a gasar matasa ta kasa, Munyal ta sanya jihar Gombe cikin taswirar wasannin motsa jiki na kasa, wanda hakan ya kara tabbatar da gagarumar rawar da ‘yan wasan jihar ke da su.
“Muna fatan yi mata tarba ta girmamawa da goyon bayan da ya dace da ita,” in ji sanarwar.
Yahaya, ya kuma yabawa iyayen Munyal da kociyoyinta kan rawar da suke takawa wajen kula da hazakar ta, tare da jaddada muhimmancin jagoranci da goyon baya a tafiyar ta na samun nasara.