Home Wasanni George Weah na yiwa ‘Super eagle’ fatan samun nasara a gasar cin kofin duniya

George Weah na yiwa ‘Super eagle’ fatan samun nasara a gasar cin kofin duniya

0
George Weah na yiwa ‘Super eagle’ fatan samun nasara a gasar cin kofin duniya
George Weah

Shugaban kasar Laberiya, George Weah, a jiya, ya bayyana cewar kungiyar kwallon kafa ta Najeriya, Super eagles ba wai kawai Najeriya zata wakilta ba a gasar cin kofin duniya da za ayi a kasar Rasha, yace Najeriya zata wakilci nahiyar Afurka ne baki daya.

Weah ya bayyana haka ne a wata tattaunawa da yayi da ‘yan jaridu na fadar Shugaban kasa, a lokacin da ya kammala ganawa da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a fadar Gwamnati dake Abuja, a jiya.

Haka kuma, SHugaba Weah ya gargadi ma’aikatar wasanni ta Najeriya, da kada ta shiga cikin lamarin kudi da ya shafi ‘yan wasa, yace duk abinda aka ware domin jin dadin ‘yan wasa, to kada ayi musu hannun jarirai, a tabbata ana biyansu hakkinsu akan kari.

Bayan haka kuma, Shugaban na Laberiya, ya nuna rashin jin dadinsa kan halayyar Shugabannin Afurka da suke nuna halin ko in kula kan batun sha’anin wasanni. Daga bisani, shugaban yayi godiya ga takwaransa na Najeriya,Muhammadu Buhari tare da yaba masa bisa nasarar da kungiyar kwallon kafa ta Super eagles ta samu na zuwa gasar cin kafin duniya da za’a buga a kasar Rasha.

Yace, ya cika da mamaki a lokacin da ya gana da Shugaban kasar Faransa, Emmanuel Macron, da yaji irin shiri da kuma tanadin da shugaban yayiwa harkar wasanni a kasar ta Faransa, ta yadda Gwamnati ta bayar da kyakkyawar kulawa kan harkar wasanni.

“Nayi aiki tukuru domin samun nasarar kungiyarmu ta kwallon kafa. Domin mu kasance cikin sahun na farko a nahiyar Afurka. Na shaidawa Macron cewar kungiyar kwallon kafa ta duniya FIFA ta gina katafaren filin wasa a Laberiya, muma kuma mun gina wani karin filin wasan a Laberiyan”

“Na san cewar kungiyar kwallon kafa ta Najeriya a shirye suke da koma waye, muna bibiyarsu a ko da yaushe. Ina iya tunawa na taka leda da kwararrun ‘yan kwallon najeriya. Amma abinda ya dace mu sani, yanzu lokacin sabbin jini ne, idan an basu dama zasu cirawa najeriya tuta”