Home Labarai Ghali NaAbba ya tona asirin kudaden da Obasanjo ya kashe don ya yi Tazarcen Karo na 3

Ghali NaAbba ya tona asirin kudaden da Obasanjo ya kashe don ya yi Tazarcen Karo na 3

0
Ghali NaAbba ya tona asirin kudaden da Obasanjo ya kashe don ya yi Tazarcen Karo na 3
Daga Hassan Y.A. Malik
Tsohon dan majalisar wakilai, Ghali Umar Na’abba ya bayyana adadin kudaden da tsohon shugaban kasa Olusegun Obaasanjo ya rabawa ‘yan majalisa a shekarar 2006 domin su bar shi ya yi mulki har iya rayuwar shi.

Ya ce kudirin baiwa shugabanni kasa damar yin wa’adi na uku ba wani abu bane illa shirin Obasanjo na zama shugaban kasa har iya rayuwar shi.

Na’abba dai na magana ne a wata hira da jaridar Punch ta yi da shi, inda ya ce Naira miliya 50 Obsanjo ya baiwa kowanne sanata da ya goyi da bayan kudirin na shi.

Ya ce ‘yan majalisar wakilai kuma Naira miliyan 40 aka basu.

Ya ce wasu daga cikin ‘yan majalisar sun karbi wadannan kudade sun kuma goyi da bayan tsohon shugaban, yayin da wasu suka ki karba.

Na’abba ya ce ya yi duk iya kokarin sa wajen ganin lamarin bai yiwu ba saboda zuciyar shi ta fada masa cewa Obasanjo ba wa’adi na uku ya ke so yi ba, so ya ke ya yi mulki har iya rayuwar shi.

Ya ce a don haka ne da shi da sauran ‘yan Nijeriya suka yi ta kamfen domin ganin ba a sauya tsarin mulkin kasar ba, ta yadda wannan manufa ta Obasanjo bata yiwu ba.