
Wata kotu a Ghana ta yanke wa mutum 12 hukuncin daurin rai da rai bayan da ta same su da laifin kisan wani soja shekaru bakwai da suka gabata.
Suna cikin mutum 14 da ake zargi da cinna wa sojan mai suna Manjo Maxwell Mahama wuta a Mayun 2017, a yankin Denkyira Obuasi, lamarin da ya tayar da kura a kasar.
Babbar kotu a Accra, babban birnin kasar ta samu mutanen 12 da laifin kisa da hada baki wajen yin kisa da kuma taimakawa a yi kisan.
Sun hada da wani dan siyasa wanda ake zargi da tattara jama’a somin kai wa sojan hari a lokacin da yake motsa jiki.
Biyu cikin wadanda ake zargi kuma an wanke su bayan da kotu ta gano ba su da laifi.
Sojan mai shekara 32 yana bakin aiki a yankin Denkyira Obuasi da ke tsakiyar kasar lokacin da mutanen suka far masa saboda zargin cewa dan fashi da makami ne.
Yana daga sojojin da aka tura zuwa yankin domin kare wurin hakar ma’adinai.
Kisan sojan dai ya fusata mutane a fadin kasar. Kuma bayan faruwa lamarin ne aka kama fiye da mutum 50 da ake zargi, sai dai bayan tantance su an tuhumi mutum 14 a cikinsu.
BBC Hausa